Kasashen Ketare

Shugaban Kasar Amurka Yaja Kunnen Masu Zanga-zangar Adawa Da Nuna Wariya A Amurka.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Shugaban kasar Amurka ya yi gargadi ga masu Zanga-zangar nuna adawa ga siyasar wariya a kasar Amurka.

A yau Asabar Donald Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, masu Zanga-zangar nuna wariya a kasar Amurka barayi ne, zaune gari banza da kuma ashararai.

Ya ce yau zai je jahar Oklahoma domin halartar wani gangami da yake da alaka da zabe, kuma ya samu labarin cewa za a yi masa Zanga-zanga, ya ce, yana kira ga masu Zanga-zangar da su kwana da sanin cewa, yadda aka bi su da lalama a biranan Minneapolis da kuma new York, ba za a yi musu haka a Oklahoma ba a yayin ziyarar tasa, yana mai yin gargadi da cewa za a dauki kwakkwaran mataki a kansu.

Tun kafin wannan lokacin Trump ya bukaci ma’aikatar tsaro ta Pentagon da ta tura sojoji domin su murkushe masu Zanga-zangar nuna adawa da siyasar wariya ta hanyar yin amfani da karfin bindiga, amma manyan hafsosin sojin kasar suka ki amincewa da hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button