Labarai

Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya goyi bayan ƙudurin dokar haraji

Spread the love

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce karancin harajin da Najeriya ke samu ya kasance wani babban cikas ga ci gaban kasar.Abbas ya bayyana haka ne a wajen gabatar da kudurin kasafin kudin 2025 ga wani zama na hadin gwiwa na majalisun taraiya da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a Abuja a yau Laraba.A cewarsa, rabon harajin Najeriya zuwa kayan da ake samarwa a kasa, GDP, a halin yanzu ya yi ƙaranci a kusan kashi 10.9 cikin 100 a 2024, inda ya ce yana cikin mafi ƙaranci a Afirka, wanda ya yi ƙasa da matsakaicin mataki na nahiyar wanda ya ke a kashi 15.6 cikin ɗari.Ya ce yawan kudin da ake tara harajin VAT a Najeriya a kusan kashi 20 cikin 100 ya yi kasa da kusan kashi 70 cikin 100 da kasashen Afirka ta Kudu, Equatorial Guinea da Zambia suka samu.Abbas ya ce, tunkarar wadannan kalubale na bukatar sauye-sauyen manufofin haraji cikin gaggawa, don fadada tushen harajin kasar, da inganta bin ka’ida, daidaita harkokin gudanarwa, da kuma rage dogaro da karbar bashi.Ya ce ‘yan majalisar za su ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Tinubu don ganin an yi gyare-gyaren da ya kamata, kuma mai inganci da kuma la’akari da bukatun marasa galihu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button