Labarai
Shugaban Tinubu Ya shirya tsaf domin Korar Ministocin da Basu yin kokari a Bakin aikin su – Hadiza bala Usman.
Shugaba Tinubu ta Baki Mai taimaka Masa Da Take lura da muhimmancin da shugaban kasa ya dora a kan cika alkawuran da ya dauka, Hadiza Usman ta ce, “Dole ne mu fahimci cewa shugaban kasa ya tashi tsaye game da alkawuran da ya dauka, kuma za a tantance ministoci, kuma ministocin za a sauke idan ba su yi aiki ba.”
Shugaba Bola Tinubu zai kori ministocin da suka kasa cika aikinsu, in ji mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin siyasa da kuma shugabar sashen isar da sako na tsakiya, Hadiza Bala Usman.
Ta yi magana ne a wajen bude taron bayar da horo na kwararru na ma’aikatun gwamnatin tarayya kan aiwatar da abubuwan da shugaban kasa ya sa a gaba da kuma abubuwan da ministocin za su samu a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.