Tsaro
Shugaban Yan Sanda Na Kano Ya Yabawa Masu Zanga Zangar #EndInSecurity A Kano
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta yaba wa masu zanga-zangar neman daƙile matsalar tsaro bisa aiwatar da ita cikin lumana.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Habu Ahmad ne ya tarɓi masu zanga-zangar, inda suka miƙa masa buƙatunsu a rubuce.
Kwamishinan ya karɓi buƙatun nasu tare da tabbatar musu da cewa za a miƙa buƙatun nasu ga hukumomin da suka dace.