Tsaro

Shugaban Yan Sanda Ya Bada Umarnin Tabbatar Da Tsaro A Yayin Zaben Gwamnonin Edo Da Ondo.

Spread the love

Sufeton yan sandan Najeriya Mohammad Abubakar yayi Kira ga Kwamishinonin Yan Sandan Jihohi 36 Na Kasar Nan da su Tabbatar Sun Karbi Duk wani makami Dake Hannun Mutane Ba bisa Ka’ida ba.

Abubakar Yayi wannan Kiran ne Yau Lahadi Inda yace, Kwamishinoni Yan Sanda Su tabbatar Sun Karbi Bindugu dake Hannun Kowa da kowa Domin Tabbatar da Tsaro a Kasar, musamman ma Lokacin da za’a gudanar da Zaben Gwamnonin Jihohin Edo da Ondo.

Sifeton yace duk wani mutum ko kungiya da ya mallaki makami ya gaggauta mikawa ga Hukuma.

Sannan yayi kira ga Kwamishinonin da su yi tarin wayar da kan al’umma a jihohin da suke Aikin domin nunawa mutane mahimmancin Zaman Lafiya Inji Shi.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button