Addini

Shugabannin Kungiyar Kiristocin Jahohin Arewa 19 Sun Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kaiwa Mabiyansu A Jihar Kaduna.

Spread the love


Daga Bappah Haruna Bajoga.


Shugabannin kungiyar kiristocin jahohin Arewa 19 sun yi ALLAH wadai da harin da aka kaiwa mabiyan su a jihar Kaduna, kuma cikin gaggawa daya daga cikin shugabannin nasu ya dira jihar Kadunar domin ganawa da Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i.
.
Dan haka kalubale a gareku shugabannin musulman Arewa, yakamata Ku dauki darasi wajen nuna damuwar Ku kuma akan kashe-kashe, da kuma zubda jinin dumbin jama’ar Ku da ake yi a sassan kasar nan Wadanda basu aikatawa kowa laifi ba, ina kuke manyan Arewa? Ina shugabannin addinin Arewa? Ina sarakunan Arewa? Idan fa kuka ci gaba da yin shiru, da nuna halin ko in kula akan yadda ake kashe muku jama’ar ku ba, to Ku sani kuma WALLAHI ba zaku tsira ba ! Ba zaku tsira b ! Ba zaku tsira ba ! Domin duk wanu abinda yaci Doma to ba zai bar Awai ba ! Saboda haka da musulmi, da kirista, da maza, da matan Arewa Ku tashi mu farka kusan bacci aiki kawai ne.
.
ALLAH ya kawo mana karshen kwararar jinin bayin ALLAH wadanda basu ji ba, basu gani ba da ake yi a kullum a Arewar da bamu da kamar ta a duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button