Siyasa

2023: Da d’umi-d’umi, Masari ya raka Dikko Radda wurin Buhari neman albarka

Spread the love

Daga | Ahmad Aminu Kado,

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ranar Litinin ya raka dan takarar Gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar APC da ya lashe zaben fitar da gwanin da jam’iyyar ta gudanar ranar Alhamis, Dr. Dikko Umar Radda wurin Buhari.

Kamar yadda Wakilin Mikiya, Ahmad Aminu Kado ya samu, Gwamnan ya raka dan takarar ne wurin Buhari domin cikon wata

al’ada da akan yi na kai dukkan ‘yan takarar jam’iyyar wurin Shugaban kasar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Dikko Radda ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC ne bayan da ya kada abokan takarar sa su takwas da kuri’u 506.

Kafin shigar sa takarar, Dikko Radda shi ne Shugaban hukumar kanana da matsakaitan sana’o’i ta gwamnatin tarayya watau SMEDAN.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button