Siyasa

2023: Idan na zama Gwamna Zan kai jihar Kaduna zuwa ga mataki na gaba kamar yadda El Rufa’i ya kafa tushe insha Allahu ~Cewar Sanata Uba sani.

Spread the love

Sanata Uba Uba sani Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Kuma Dan takarar Gwamnan jihar kaduna a Karkashin jam’iyar APC Mai Mulki ya Fadi Hakan a jiya gidan Kashim Ibrahim Yana Mai cewa

Na kudurin aniyar daukaka Jihar Kaduna zuwa ga kololuwar mataki na gaba ta hanyar dorewa da gina kyawawan abubuwan da gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai ta gadar mana idan na zama Gwamnan jihar. Na yi alƙawarin tafiyar da gwamnati ga ci-gaban jama’a da haɗa kai. Shuwagabannin kananan hukumomi da masu unguwanni da shuwagabannin jam’iyya da ‘ya’yan jam’iyya a kananan hukumomi 4 sun dukufa wajen ci gaba da gudanar da ayyukana tare da kudurin yin gaggawar tuntubar sauran ‘yan jam’iyyar domin kara fadadawa da zurfafa sakonmu zuwa ga Al’ummar jihar ta Kaduna.

Sanatan ya yabawa mahalarta Taron inda kare da cewa Ina mika godiya ta musamman ga tsofaffin ‘yan majalisar tarayya, masu rike da mukamai da tsofaffin ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna, shugabannin kananan hukumomi na yanzu da na baya, da manyan jami’an gwamnati da shugabannin mata da suka yi min rakiya zuwa kananan hukumomi 4 da suka yi min rakiya a kokarina na neman kujerar Gwamnan Jihar Kaduna. Masu rakiyar sun hada da.

(1) Hon. Abubakar Mamadi (tsohon mamba, National Assembly)
(2) Hon Bashir Zubairu (Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna).
(3) Hon. Aminu Shagali (Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
(4) Hon. Ahmed Chokali (shugaban masu rinjaye, majalisar dokokin jihar Kaduna)
(5) Hon. Yakubu Soja (tsohon mamba, majalisar dokokin Kaduna
(6) Hon Hayatu Usman (Tsohuwar ‘yar majalisar dokokin jihar Kaduna)
(7) Hon. Aliyu Idris (Council Chairman, Zaria LG)
(8) Hon. Kabiru Jarimi (Council Chairman Kaduna South LG)
(9) Hon. Abubakar Buba (Council Chairman Lere LG) (10) Hon. Bashir Zuntu (Council Chairman Kubau LG) (11) Hon. Muktar Baloni (Council Chairman, Kaduna North LG)
(12) Hon. Jaja (Council Chairman, Kudan LG)
(13) Hon. Abubakar Shehu (Council Chairman, Giwa LG)
(14) Hon. Abubakar Master (Tsohon Chairman Sabon Gari LG)
(15) Hon. Naziru (Mataimakin shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa).

Wasu kuma (16) Arch. Sani Abbas (memba, kwamitin shugaban kasa akan mai da iskar gas)
(17) Engr. Namadi Musa (tsohon DG, Bureau for Inter Religious Affairs).
(18) Hajiya Rabi Salisu (Uwar Marayun Zazzau)
(19) Hon. Ibrahim Shehu Haske (mai ruwa da tsaki na jam’iyyar, Giwa LG
(20) Dr. Fatima Zuntu (ma’aikaciyar lafiya)
(21) Hajiya Hafsat (dan jam’iyya)
(22) Salisu Ayaga (mai ruwa da tsaki, Kaduna ta Kudu LG) (23) Bala Danja (mai ruwa da tsaki na Kaduna ta Kudu LG)
(24) Baba Lere (mai ruwa da tsaki, Jama’a LG).

Sanata Uba sani dai shine Dan takarar Gwamna Mafi kwarjini da karfin tarin jama’a mabiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button