Siyasa

Akwai yiwuwar Gwamna mai jiran gado a Jihar Kaduna ta kasance Ƴa-mace. ~Cewar Gwamna Nasiru El-Rufa’i

Spread the love

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Gwamna Nasiru Ahmed El-Rufa’i na Jihar Kaduba ya bayyana cewa yana ji a ransa wannan karon Mace ce za ta zama Gwamniya a Jihar Kaduna a zaɓe mai zuwa.

El-Rufa’i ya bayyana haka ne a yau Talata yayin amsa tambayoyi na musamman daga ƴan Jaridu a Jihar Kaduna. Ya ce, “akwai yiwuwa da kaso 50% wanda yake ji a ransa cewa Mace zata zama Gwannan Jihar ta Kaduna.

Gwamman wanda a halin yanzu yake jagorantar Jihar tare da taimakon mataimakiyarsa wato Dr Hadiza Balarabe, ya ƙara da cewa Gwamnatin ta Jihar Kaduna, za ta cigaba da baiwa mata damarmaki wajen taka irin ta su rawar a gwamnatance.

Kamar yanda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito, El-Rufa’i, ya kuma yi kira na musamman ga sauran al’ummar Nigeria akan su baiwa mata da matasa dama ta fannin shugabanci domin hakan zai kawo cigaban ƙasa.

A ƙarshe, yayi addu’ar neman taimako daga Allah, akan Ya zaɓawa al’ummar Kaduna mutum nagari wanda zai kyautata rayuwar al’umma, tare da gyara kurakuran da yayi domin cigaban Jihar Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button