ANA-WATA-GA-WATA: PDP ta dakatar da Ambasada Aminu Wali

Tsohon ministan ƙasashen waje Ambasada Aminu Wali ɗan jam’iyyar PDP ne, kuma daga mazaɓar Hotoro yake. Reshen jam’iyyar PDP ɗin ne dai ya dakatar da tsohon ministan har na tsawon wata shida.

Wannan ya biyo bayan wata takarda da jam’iyyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaba da kuma sakataren na jam’iyyar a mazaɓar Hotoro ta Kudu.

Kamar yadda jam’iyyar ta bayyana, dakatarwar ta samo asali ne sakamakon gaza bayyana a gaban kwamitin da jam’iyyar ta kafa akansa ne.Jam’iyyar ta bayyana cewar, ta ɗauki wannan matakin kin ne, badon son bataso ba, a’a sai domin gazawa da shi Aminu Walin yayi na ya bayyana a gabanta domin ya kare kansa daga zargin da ake masa, wanda hakan yasa bata da wani zaɓi face ta dakatar dashi har na tsawon wata shida cif-cif.

Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *