Ana wata ga wata: PDP ta kori tsohon Ambasadan wajen Nigeria

Jam’iyyar PDP a jihar Kano, ta dakatar da tsohon Ambasadan wajen Nigeria, Amb Aminu Bashir Wali, daga cikinta har tsawon watanni shida masu zuwa, tun daga kan mazaba zuwa karamar hukuma har zuwa matakin jiha, biyo bayan gaza bayyana da yayi a gaban kwamitin bincike da jam’iyyar ta kafa kan wasu zarge zarge da ake masa, na yiwa jam’iyya zagon kasa.

Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, jam’iyyar ta PDP tace tayi duba ne akan sashi na 58 (1) (a) da kuma (I) cikin baka, sai kuma sashi na 59 (1) (d) cikin baka, na kundin tsarin mulkin PDP wanda aka yiwa gyara a shekarar 2012, kamar yadda sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP reshen karamar hukumar Nasarawa, Sulaiman Mainasara, ya bayyana.

A wannan tsakanin dai, jam’iyyar PDP a jihar Kano, ta dakatar da guda cikin dattawanta na karamar hukumar Nasarawa, Alhaji Yahaya Bagobiri, sai kuma tsohon sanatan Kano ta Arewa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo, wanda shima jiya muka samu sanarwar dakatar dashi tsawon watanni shida, kamar yadda muka samu sanarwa daga sakataren watsa labaran jam’iyyar PDP na karamar hukumar Gwarzo, Shaddadu Danjuma Aliyu Gwarzo.

Daga: Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *