Atiku Ya Nada Saraki da Shekarau, Da Sauransu A Matsayin Masu bashi Shawara a fagen yakin neman zaben sa.

Gabanin fara yakin neman zaben 2023 a ranar Laraba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya nada manyan mashawarta na musamman da nufin karfafa tawagar yakin neman zabensa na shugaban kasa.

Wadanda aka nada sun hada da tsaffin shugabannin majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki a matsayin mashawarci na musamman ga dan takarar shugaban kasa da kuma Sanata Pius Anyim a matsayin mai ba shi shawara na musamman.

Sauran wadanda aka nada a matsayin mashawarta na musamman ga dan takarar sun hada da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da kuma Sanata Ehigie Uzamere.

An kuma nada tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus a matsayin mai baiwa dan takarar shugaban kasa shawara a fannin fasaha.

Nadin da zai fara aiki nan take.

Atiku Abubakar ya bukaci wadanda aka nada su yi amfani da kwarewarsu ta siyasa wajen ganin cewa yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya samu gagarumar nasara a zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *