Siyasa

Ba Za Ku Yi Kirsimeti Na Gaba A Kan Layukan Man Fetur ba – Atiku

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin cewa ba za su kara yin jerin gwano na layin mai ba gidajen yayin bikin Kirsimeti idan suka zabe shi a watan Fabrairu.

Atiku ya bayyana haka ne a sakonsa na Kirsimeti wanda mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa Phrank Shaibu ya sanya wa hannu.

Ya ce gwamnatin APC ta kafa sabon tarihi na karancin man fetur mafi dadewa a tarihin Najeriya.

Shaibu ya lura cewa karancin man fetur din da ya fara a watan Janairun 2022, saboda shigo da gurbataccen man fetur ya ki sauka.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Yayin da karancin man fetur ke ci gaba da wanzuwa har zuwa watan Disamba, gwamnati ta kaure da uzuri duk da cewa mafi yawan ‘yan Najeriya a halin yanzu suna cikin halin kaka-ni-kayi ga ‘yan kasuwa masu sayar da man fetur da ya kai Naira 500 kan kowace lita. Kamfanin mai na NNPC wanda shi ne mai shigo da man fetur shi kadai ya kasa gudanar da ayyukansa, hakan ya nuna karara cewa mayar da man fetur din nasa na kwaskwarima ne kawai.

“Amma babban mai laifi a cikin wannan rikici shine shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda shine ministan man fetur. Abin bakin ciki ne yadda ya kasa kawo tallafi ga ‘yan Najeriya da ke fama da tabarbarewar hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da rashin tsaro.

“Abin takaici ne yadda Tinubu ya yi alkawarin cire tallafin mai a lokacin da jam’iyyarsa ta rike shi tsawon shekaru bakwai da kuma kashe biliyoyin daloli wajen tallafa wa masu aikata laifuka. A bayyane yake cewa furucin Tinubu zargi ne akan Buhari.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button