Siyasa

Ba zaka ku sake Jin yunwa ba matukar muka lashe zaben shugabancin Nageriya na 2023 ~Cewar Mataimakin Atiku Okowa.

Spread the love

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta Sen. (Dr) Ifeanyi Okowa ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi Atiku Abubakar da dukkan ‘yan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 don tabbatar da cewa yunwa, fatara da rashin tsaro da suka mamaye kasar an kawar da su.

Okowa ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis din da ta gabata a wajen yakin neman zaben jam’iyyar a kananan hukumomin Oshimili ta Arewa da Oshimili ta kudu na jihar, ya kuma ce gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta mayar da ‘yan Najeriya baya.

Ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta lalata tsarin zamantakewa da tattalin arzikin kasa, ciki har da bangaren ilimi inda gwamnati ta baiwa malaman jami’o’i damar shiga yajin aikin na tsawon watanni takwas.

A cewarsa, saboda Allah ya ba ni izinin tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa kuma ya dora ni a tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya gama mana wannan aikin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button