Siyasa

Babbar Magana: Rarara bai gayawa Ganduje bakar magana ba, magoya bayan Ganduje da sauran jama’a ne basu fahimci ma’anar kalmar “Hankaka” ba

Spread the love

Mawakin Siyasa na Jam iyar APC Mai mulkin Dauda Kahutu Rarara ya musanta cewa ya gayawa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bakar magana acikin Sabuwar wakar sa ta hankaka.

Rarara ya ce Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da magoya bayansa da sauran Jama’ar Jihar Kano ne basu fassarar abin da Kalmar hankaka take nufi ba, shiyasa suke ganin kamar ya wulankanta Gwamnan Jihar ne.

Kahutu Rarara ya ce abinda yake nufi da hankaka Shine.

” Hankaka Maida Dan wani naka, kowa yaga farinka sai ya ga bakinka.”

Ya ce Wannan ba wata kalma bace baqa Mai zafi ba, mutane ne basu fahimceta ba.

Wannan bayanin na Dauda Kahutu Rarara ya fito ne tabakin wani Babban yaron sa dake zaune a karamar hukumar Dala Mai suna Abdurrashid Sa’adu,Wanda yana cikin masu yi masa kida da Jita, Wanda ya nemi kada a Dora hotun sa.

To Allah ya kyauta.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button