Babu sa hannu na a tallafin shinkafa da ake rabawa a Arewa. -Tinubu

Tsohon Gwamnan Lagos kuma jigo a Jam’iyyar APC ya bayyana cewa babu sa hannunsa a tallafin shinkafar da ake rabawa ga talakawa kwanan nan a wasu jahohin Arewacin Nigeria “face sai dai ƙoƙari na wasu ƙungiyoyi wanda sukayi amfani da sunansa”.

Mista Tinubu ya bayyana haka ne a wani ɗan takaitaccen bayani nasa da kamfanin dillacin labarai na News Agency of Nigeria (NAN) suka wallafa; wanda ya fito ta hannun Mataimakinsa na musamman a shafukan sada zumunta, mai suna Tunde Rahman.

NAN sun ƙara da cewa; a kwanakin baya-bayan nan ne dai aka ga hotunan fuskar Tinubun ɗauke a jikin buhun-hunan shinkafa ana rabawa saɗiƙan wanda hakan ya ɗauki hankalin mutane matuƙa, har ya sanya wasu suke ganin hakan a wani salon fara yaƙin neman zaɓe da Tinubun ya soma.

Yayinda a gefe gud shi kuma tsohon gwabnan ya keɓance kansa da ɗaukar nauyin wannan tagomashi.

A ƙarshe ya bayyana cewa; ba shine ya ɗauki nauyin wannan aiki ba, amma ya yabawa ƙungiyoyin da suka ɗauki wannan nauyi na bada tallafin abinci ga masu ƙaramin ƙarfi musamman a irin wannan wata na Ramadan

Daga Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *