Badaru ya buɗewa matasa ƙofar samun mulki

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar Talamiz Ya Tsayar Da Matasa Takarar Shugabannin Ƙananan Hukumomi

A yayin da matasan Najeriya ke kiraye-kiraye, kwarmato da tada jijiyoyin wuya don ganin an dama da su a harkokin siyasa, duk da rattaba hannu da Maigirma Shugaban Ƙasa ya yi na samar da ƙudurin dokar da Majalisar Ƙasa ta samar domin baiwa matasa damar tsayawa takara a matakai daban-daban, a Jihar Jigawa kuwa abun a aikace yake, domin Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar bayan amincewa da dokar, sai da ya tabbatar da baiwa matasan gurabe na tsayawa takara a matakai daban-daban na mulki.

Zamu tabbatar da hakan, bisa la’akari da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanaye a zaɓen cikin gida na matakin farko, wanda Jam’iyya mai mulki ta APC ta gudanar a baya bayan nan, a shirye-shiryen da take yi na tunkarar zaɓukan ƙananan Hukumomi da za’a gudanar a Jihar Jigawa, inda zaƙaƙuran matasa masu jini a jika, irin su Ahmad Rufai Gumel wanda ya samu sahalewar Jam’iyyar na tsaya mata Takarar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gumel, Bala T. O. wanda zai yi Takarar Shugaban Ƙaramar Hukumar Hadejia, Bala Usman Chamo wanda zai yiwa Jam’iyyar Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Dutse, Lawal Isma’il wanda zai yi takarar ƙaramar hukumar Ɓaɓura, Mudassir Musa wanda zai yi takarar ƙaramar hukumar Garki, Mubarak Ahmad wanda zai yi takarar ƙaramar hukumar Ƴankwashi inda waɗannan kaɗan daga cikin sauran ƴan takara matasa da ɗaruruwan sauran matasan da zasu tsaya takarar Kansiloli a Ƙananan Hukumomi na mulki 27 dake faɗin Jihar Jigawa.

Ko a taron muryar talaka na wannan shekarar sai da gwamnan ya yi hannunka mai sanda akan yadda ya ke ƙoƙarin ganin matasa sun samu madafin iko a jihar.

A yanzu dai, al’ummar ƙananan waɗannan hukumomi cike suke fatan ganin wadannan matasan da aka basu wannan damar sun baiwa marar ɗa kunya.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *