Bauchi: APC ta ki yarda da kayan tallafi na Azumi da Bala Mohammed ya bayar

Jam’iyyar All Progressive Congress, APC reshen jihar Bauchi ta yi watsi da kayan abinci da Gwamna Bala Mohammed ya bayar don magance matsalolin azumin watan Ramadana.

Kayan abincin, kamar yadda suka zo, sun hada da shinkafa, masara, sukari, spaghetti da dawa 

An kai kayayyakin ga sakatariyar jam’iyyar a ranar Laraba amma jami’an jam’iyyar suka ki.

Da yake magana da dan rahoto, Sakataren yada labarai na APC, Adamu Aliyu-Jallah, ya dage cewa ya saba wa al’adar APC karban irin wannan daga Gwamna na PDP.

Malam Aliyu-Jallah ya ce: “Mu kwamatin aiki na reshen APC mun ki amincewa da shi saboda matsalar ita ce idan muka amshi wadannan kaya daga gareshi za a yi mana fassara ta daban da ita.

“Na biyu, Ramadan din da ya gabata, ba su kawo shi ba to me ya sa yanzu? Bayan wannan, akwai ma’aikatan da har yanzu ba a biya su albashin su ba.

“Ya kamata su ba su, ko da an ba mu tirela 100 na shinkafa, ba zamu karba ba saboda haka bawai mun duba yawan kayan da suka kawo bane a matsayin kayan Azumi a gare mu ba.”

Ya kara da cewa: “Sun kawo ragowar kayan taimako na COVID-19 da aka rage a sakatariyar jam’iyyarmu da misalin karfe 1:00 na rana a ranar Laraba a matsayin kayan tallafin azumin Ramadan kuma wadanda suka kawo shi sun ce daga Gwamnan Bauchi ne amma hakan ya saba wa al’adar jam’iyyarmu.

“Ba za mu iya karbar komai daga jamiyyar mai adawa ba, saboda haka babu wani dalili da za su ba mu komai.”

Daga Maryam Ango

0 thoughts on “Bauchi: APC ta ki yarda da kayan tallafi na Azumi da Bala Mohammed ya bayar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *