Bayan Buhari ya gama: Zakaji Ana cewa:

 1. Shine ya ida ginin Second Niger Bridge
 2. Shine ya sake Gina hanyar Abuja-Kaduna-Kano
 3. Shine ya Gina Layin Jirgi na Ibadan zuwa Lagos
 4. Shine ya Gina Layin Jirgi na Itakpe zuwa Warri
 5. Shine ya sake Gina hanyar Kano-Maiduguri
 6. Lokacinsa ne muka fara ganin shinkafa yar gida a cikin buhu kamar yar waje
 7. Lokacinsa ne aka fi samun wutar lantarki tunda aka dawo mulkin dimokradiyya
 8. Shine ya Gina Layin Jirgi daga Kano-Kazaure-Katsina-Maradi
 9. Shine ya Sanya bututun iskar gas tun daga Kogi har Kano
 10. Shine ya ida ginin hanyar Kano-Katsina ya kuma mai data hannu biyu
 11. Shine ya ida aikin ruwan sha na zobe Dam, daga Dutsinma zuwa Katsina
 12. Shine Ya ida aikin layin Jirgi na Kaduna zuwa Abuja
 13. Lokacinsa aka ida gyaran Airport ta Enugu
 14. Lokacinsa ne aka Gina Army University a Biu ta Jihar Borno
 15. Lokacinsa ne aka Gina Jamiar Sufuri ta Daura
 16. Lokacinsa ne aka Gina Makarantun Kimiyya da Fasaha na Kaltungo da Daura
 17. Lokacinsa ne aka Gina Jamiar Ilmin kimiyyar lafiya a Utukpo dake Jihar Benue
 18. Lokacinsa ne aka sake Gina hanyar Zaria-Funtua-Gusau
 19. Lokacinsa ne aka dauki matasa 500,000 ake basu N30,000 duk wata har na tsawon shekara 2 a tsarin N-Power
 20. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren bada bashin noma da ake cema Anchor Borrowers Program don inganta harkar noma a Arewa da Nigeria
 21. Lokacinsa aka fi daukar maaikata a kowane bangare na Gwamnati
 22. Lokacinsa ne ya Sanya hannun kan dokar cin gashin kai ta Kananan Hukumomi, yan majalissun jihohi da bangaren sharia na jihohi Amma gwamnoni suka ki aiwatarwa kuma jama’a su kayi shuru.
 23. Lokacinsa ne ya sake Gina hanyar Ibadan zuwa Lagos.

Kadan kenan.

Ahmad Aminu Kado…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *