Bikin karamar Sallah: Buhari ya bukaci yan Najeriya da su dage da addu’a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 12 ga watan Mayu, ya roki ‘yan Najeriya da su yi addu’a a kan satar mutane, fashi da makami da batanci.

A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya yi kiran ne a sakonsa na Eid-il-Fitr wato bikin karamar Sallah.

An sanya wa sanarwar take da ‘A yayin bikin Idi, Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai’.

Shugaba Buhari ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kiyaye dukkan matakan rigakafin na COVID-19 da yin biki yadda ya kamata yayin hutun.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *