Siyasa

Bikin Sallah: Ahir ɗin Ku da Ɗaga Allunan Siyasa da liƙa Hotuna a Wajen Bikin Sallah — Ganduje.

Spread the love

Da alama dai wannan ƙaramar sallar zata zo da sabon salo a siyasance.

Domin kuwa zancen da ake yi yanzu haka, Mai girma gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya hana liƙa duk wani hoto na siyasa, ɗaga shi ko kuma wata alama da zata nuna ɓangarancin siyasa.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba, shine ya fitar da wata sanarwa mai ɗauke da wannan batu a yau a madadin gwamnan.

Gwamnan na jihar Kano yace, daga rana irin ta yau, indai taron sallah za’a yi, an hana saka tutoci da allo irin na siyasa sa’ilin da ake gudanar da sallar idi da kuma sauran tarurruka da suke da alaƙa da bikin sallah, saboda dai a samu a gujewa rikici.

Gwamnan na Kano yace, sallah dai ibada ce a Musulunci mai muhimmanci da akeyi bayan azumin watan ramadana, gamida baje koli irin na al’adu , wanda hakan ke janyo baƙi daga ko ina a faɗin duniya da suke zuwa buɗe ido jihar Kano.

A cewar Gwamnan, dalilin haka ne yasa bai kamata a mayar da irin wajajen nan wurin gangamin siyasa da yaƙin neman zaɓe ba.

Sanarwar bugu da ƙari, ta bawa ƴan siyasa umarni dasu tabbatar da cewa sun yi biyayya sau da ƙafa ga wannan sabuwar dokar ta zaɓe.

Daga ƙarshe, gwamnan jihar Kanon ya taya ɗaukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar sallah Ƙarama, tare da fatan za’a cigaba da kwatanta halaye nagari da aka koya a watan mai albarka.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button