BOKO HARAM: Gwamna Mai Mala Ya Bada Tallafi Na Agajin Gaggawa A Fadin Jihar Yobe

Gwamnatin jihar Yobe, ta fadada tallafin gagawa tsakanin al’ummar jihar, tun bayan faruwar rikicin yan ta’addan Boko Haram a garin Geidam, inda dubun-dubatan mutane suke gudu suke barin gidajen su da dukiyoyin su domin tsira da rayukan su.

Gwamna Mai Mala Buni karkashin hukumar agajin gaggawa ta jihar Yobe, wanda kulawarta yake karkashin Dr. Muhammed Goje, tun bayan makon daya gabata ta fadada aiyukan jin kan al’ummar jihar, domin tallafawa mutanen da suka baro gidajen su, sanadiyar rikicin fadan ‘yan ta’addan Boko-Haram da suka shiga garin.

YOSEMA tana bibiyar duk lungu da sako na fadin jihar, domin neman mazauna garin Geidam, wanda suke zaman hijira a wasu sassa na jihar Yobe, domin taimaka musu da kayan abinci, abin kwanciya, da abubuwan da suka shafi rayuwar na dole.

Yadda Gwamnatin jihar ta dage dantse wajen ganin ta tabbatar da taimakawa mutanen da rikin ‘yan ta’addan ya rabosu da gidajen su, cikin Wannan watan Azumi, haka hukumar ta fantsama take bi gari-gari, kauye-kauye domin zakulo mutanen ta taimakawa musu dan rage musu zafin radadin abinda ya fara.

Hukumar ta bude kofafin taimakawa masu gudun hijira, domin rage musu zafin radadin rabuwa da gidajen su, da dukiyoyin su,

Muna addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a jihar mu ta Yobe da Nijeriya baki daya.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *