Boko Haram: Ndume Ya Tona Daga Inda Yan Ta’adda Ke Samun Makamai da Alburusai

Sanata Ali Ndume ya bayyana daga inda ‘yan kungiyar Boko Haram ke samun makamansu –

A cewar tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan, masu tayar da kayar bayan suna sace makamai da alburusai daga sojoji da hukumomin tsaro

Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka watsa a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan Sojoji, ya magantu a kan tushen makaman Boko Haram da ake yawan amfani da su don aiwatar da ta’addanci.

Ndume ya yi ikirarin cewa yawancin makamai da alburusai da maharan ke yin amfani da su an sace su ne daga wajen sojojin Najeriya, rundunar tsaro, da sauran hukumomin tsaro.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin din Channels TV Politics Today wanda aka watsa a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu.

A cewarsa, masu tayar da kayar bayan suna kan neman kayan yaki da alburusai bayan shugaban sojojin ya kunna musu wuta.

Ya ci gaba da bayanin cewa ‘yan ta’addan kuma suna samun makamai daga Libya da Chadi.

Lokacin da aka tambaye shi ko ‘yan ta’addan da suka mamaye wasu yankuna na arewa maso gabas koma baya ne, Ndume ya ce ba haka bane.

Ya bayyana cewa masu tayar da kayar bayan sun rike garuruwan ne sakamakon karancin sojoji a kasa.

Da yake ci gaba da magana, dan majalisar ya bayyana cewa kungiyar ta’addancin ba ta rike wani gari har abada.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *