Buhari ya bada sanarwar fadada shirin N-Power domin ‘Ya ‘yan Talakawa su amfana

Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda ta taimakawa matasa da marasa galihu – Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an ribanya adadin masu yin aikin N-Power.

Yanzu matasa miliyan daya za su ci moriyar shirin N-Power da aka fito da shi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta fadada wadanda za su mori tsarin N-Power da aka shigo da shi, domin matasa su amfana.

Jaridar PM News ta ce Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yanzu za a kara adadin matasan da su ke cikin wannan tsari daga mutum 500, 000 zuwa 1, 000, 000.

Shugaban kasar ya yi wannan bayani ne a jawabinsa da ya fitar domin taya al’umma murnar ranar ma’aikata ta kasa a ranar Asabar, 1 ga watan Mayu, 2021.

Muhammadu Buhari ya ce fadada tsarin N-Power zai taimaka sosai wajen samar da aikin yi da yaki da talauci a lokacin da ake fama da annobar COVID-19.

Gwamnatin tarayya ta kawo wannan shiri na N-Power ne a 2016 domin inganta rayuwar matasa.

Shugaban kasar ya ce an fadada tsarin tattalin arziki da zamantake wa na bada kudi a gidaje miliyan 7.6 daga gidaje miliyan 2.6 na marasa galihu da aka yi a da.

Da wannan shiri, mutane miliyan 32 za su amfana da gwamnati, akasin miliyan 13 da su ka mora a baya.

Bayan haka gwamnati ta shigo da tsarin bada tallafin COVID-19 RRR wanda zai tallafa wa talakawa da masu karamin karfi akalla miliyan 20 da ke birane.

Sannan kuma ma’aikatar masana’antu da zuba jari da kasuwancin tarayya ta shigo da tsare-tsaren bada jari da zai taimaka wa kananan ‘yan kasuwa a kasar.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *