Buhari Ya Fi Ka Draja – Wata Kungiyar Dattawa Ta Fadawa Obasanjo.

Wata kungiyar dattawa a karkashin inuwar kungiyar dattawan kishin kasa (PEC), ta yarda cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi Olusegun Obasanjo tsari a kan harkokin mulki a Nijeriya.

Kungiyar karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Ari Gwaska da Cif Simon Shango sun ce nasarorin da Shugaba Buhari ya samu kan harkar tsaro ya zarta wadanda magabatansa suka samar.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, kungiyar ta bayyana kalaman da Obasanjo ke bayyana Najeriya a matsayin kasar da ta gaza a matsayin “karya”.

Kungiyar dattawan ta ce shugaba Buhari ya tsaya kan hadin kan kasar da rashin rarrabuwa a kowane lokaci.

Yayin da kuma ta yarda cewa Obasanjo ya cancanci girmamawa bisa matsayinsa na tsohon shugaban kasa da tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, kungiyar ta ce kalaman nasa mafi yawan lokuta ba daidai bane.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Halin da Najeriya ke ciki kamar yadda Shugaba Buhari ya gada ya bayyana shi da sauki ya kasance mummunan abu, mai ban tsoro da takaici.

Babu wani rashin nasarar shugabanci a kasar da zai iya sauka kasa.”

Dattawan sun ce kalaman da Obasanjo yayi game da halin da kasa ke ciki yaudara ce.

Ta yabawa shugaban bisa kokarin da yayi, kungiyar ta bukaci shugaba Buhari da kar ya taba shagala; amma ci gaba da hangen nesan sa kan hanya don ceton al’ummar daga kango.

“Cif Obasanjo ba zai iya musantawa ko musanta irin sadaukarwar da sojojin Najeriya suka yi ba domin maido da zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar da ke fama da rikice-rikicen kungiyar Boko Haram, ‘yan bindiga masu dauke da makamai da barayin shanu a yankin arewa maso yamma, da ta’addancin tsagerun Neja Delta da duk wasu rikice-rikicen da ke faruwa wadanda suka mamaye tsaron jama’a suka kuma sanya ‘yan Najeriya bakin ciki, “in ji dattawan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.