Buhari yayi alkawarin aiki da Nijar wurin daidaita ECOWAS. 

A ranar litinin, shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar ma sabon shugaban kasar Mohammad Bazoum cewar Nigeria a shirye take da tayi aiki da kasar domin a samu daidaituwar kasashen Afrika ta yamma. 

Buhari a yayin da ya amshi bakuntar Bozoum a Vila a Abuja, ya tabbatar mai da cewa Nijeriya zatayi komai domin taga cewar “an samu daidaituwa don cigaban kasashen guda biyu”

Buhari yayi nuni da cewa yan Nijar da Nijeriya mutane ne masu dangantaka wurin yare da al’adu da kuma hanyoyin rayuwa.

Sannan kuma ya dada da cewa “mun hada kasa ta boda adadin kilomita dubu daya da dari biyar don haka bazamuyi watsi da juna ba”

Kashashen biyu kuma sun zamanto suna fuskantar matsalolin hare hare daga wurin (ISWAP) da kuma boko haram wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da hijirar wasu.

“ka dade kana cikin wannan tsarin, abinda baka taba yi ba shine shugabancin kasa, yanzu kuma ka zama” inji Buhari.

Ya kuma tabbatar mai da cewa Nijeriya zata taimakawa Nijar a wurare daban daban a inda aka bukaci taimako.

“Akan kuma ta’addanci da ke tahowa daga Boko Haram, Buhari ya lura cewar ita Nijar din ta kalubalanta sosai.

“Zamuyi duk abinda ya dace domin ganin mu kare wadan nan kasashen namu guda biyu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma mika godiya ga shugaban kasar Nijar daya gabata kafin Bazoum, Muhammadu Isoufou, inda yace shugaban yayi kokari sosai wurin ganin an samu daidaituwa sannan yayi kira ga sabon shugaban kasar da ya cigaba da aikin da wanda ya gabata gareshi ya dasa.

Shugaba Bozoum yace yaji dadi daya fara ziyartar Nijeriya kuma ya gano cewar suna da abubuwa da dama iri daya wanda suke son cimma buri saboda haka, mu’amala mai kyau tsakanin kasashen biyu nada matukar muhimmanci.

Akan tsaro, ya lura cewar mutanen Nijeriya da dama sun gudu kasar Nijar lokacin da aka kai hare hare, “Wannan yana nuna cewar yakamata mu hada kai domin mu fuskanci kalubalen mu tare da yaki da su”

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *