
A wani Rahoto da POLITICS DIGEST suka wallafa na Cewa amu cewa burin takarar zama gwamna na Murtala Sule Garo a jam’iyyar APC ya ruguje, inda aka ce Gwamna Abdullahi Ganduje na fuskantar matsin lamba kan ya cire shi a jerin matsayin wanda zai gaje shi.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnan ya tafi kasar Hadaddiyar Daular Larabawa domin wani taron zuba jari wanda kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) suka gudanar.
Garo wanda a halin yanzu shi ne Kwamishinan Kananan Hukumomi a Jihar, a cewar majiyoyin, yana jiran amincewar Gwamnan ne kafin ya mika takardar murabus dinsa.
A ranar Alhamis ne Garo ya tashi zuwa kasar Dubai da kansa domin neman karin haske daga wurin gwamnan.
“Abin da ke kawo jinkirin murabus din shi ne haryanzu bai da tabbacin ko gwamnan zai mara masa baya. gwamnan yana magana daga bangarorin biyu kuma matsin lamba daga sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zai sa gwamnan ya canja ra’ayinsa kan Murtala.
“Baffa Babba Dan-agundi yana Dubai shima, Garo na iya jin dadin ganin gwamna tare da Dan-agundi wanda ke kan gaba wajen goyon bayan wani dan takarar gwamna mai karfi, Kabiru Rurum.
“Ina ganin wannan ne ya sa ya yi tafiya domin ya gana da gwamnan domin samun tabbaci da goyon bayan Gwamnan,” inji majiyar.
Garo yana daya daga cikin manyan jami’an gwamnati a wannan gwamnati. Ya samu amincewar uwargidan gwamnan, Hajiya Hafsat Ganduje, a lokacin wani shirin karfafa gwiwa a Bichi a shekarar da ta gabata Hafsat Ganduje ta taba ambata cewa ire iren su murtala gari ne ya dace su gaji Dr Abdullahi Umar ganduje a zaben 2023 lamarin daya kawo Cece kuce.