Da Ɗuminsa: Ahmad Lawan Ya rantsar da sabon sanata

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya rantsar da sabon mamba a majalisar yau, wanda aka zaɓa daga mazaɓar sanatoci dake Imo ta arewa

An rantsar da sabon sanatan ne bayan gudanar da zaɓen maye gurbi kuma ya samu nasara a mazaɓar tasa ƙarkashin jam’iyyar APC

Frank Ibezim, shine zai maye gurbin tsohon sanata, marigayi Benjamin Uwajumogu, wanda ya rasu a shekarar data gabata

Kuma hukumar zaɓe ta gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar tun wasu yan watanni da suka gabata.

Tun a lokacin hukumar zaɓe ta sanar da jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaɓen, sai-dai rikicin cikin gida yasa ba’a rantsar da wanda ya samu nasarar ba.

Lamarin ya jawo kace-nace tsakanin Ifeanyi Ararume da kuma Ibezim, inda kowa ke iƙirarin shine halastaccen ɗan takara a ƙarkashin jam’iyyar APC ɗin.

Rikicin dai saida yakai gaban kotun ƙoli, wadda daga ƙarshe ta ayyana Frank Ibezim a matsayin ɗan takarar APC kuma wanda ya samu nasara a zaɓen cike gurbin da ya gabata.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *