DA DUMI-DUMI: Buhari na tare da Pantami dari bisa dari ba za a sauke shi ba, kuma Gwamnati tarayya zata hukunta masu bata masa suna –inji fadar Shugaban kasa

Fadar Shugaban kasa ta ce Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana tare da Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami kuma ba zata sauke shi ba kamar yadda wasu ke ta kiraye-kirayen a sauke shi.

Manuniya ta ruwaito kakakin Shugaban kasa Garba Shehu a wata sanarwa yana mai cewa zuwan Dr Isa Ali Pantami a matsayin minista ya kawo cigaba da sauye-sauye da yawa da ba zasu kirgu ba wanda miliyoyin yan Nigeria ke amfana dasu a kowace rana.

Sanarwar ta ce wasu ne kawai suke yiwa ministan bita da kulli suna dangantashi da ta’addanci, Garba ya ce sun samu rahoton yadda wasu kamfanonin sadarwa bata gari suka ware makudan kudade suka kai gidajen jaridu domin a batawa ministan suna amma sai jaridun suka ki karba, ya ce fadar shugaban kasa na bincike kan lamarin kuma zata hukunta duk wanda ta kama da hannu a ciki.

A karshe ya ce Gwamnatin tarayya ta Muhammadu Buhari suna tare da Ministan dari bisa dari

Wannan dai ya kawo karshen rade-radin da ake yi da kiraye-kirayen cewa sai Buhari ya sauke ministan

Daga: Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *