Da Dumi Dumi: EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Okorocha.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta damke tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

Daraktan yada labarai na hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya fadawa jaridar The PUNCH a ranar Talata cewa an kama Okorocha a Abuja.

Uwujaren, ya ki cewa komai game da dalilin kame Sanatan da ke wakiltar Gundumar Sanatan Imo ta Yamma.

Lokacin da aka tambaye shi, jami’in na EFCC ya ce, “Gaskiya ne, an kama (Okorocha) yau a Abuja amma ba mu bayar da cikakken bayani.”

Cikakkun bayanai za su zo daga baya…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *