Siyasa

Da ‘dumi ‘dumi: Ganduje ya Chanja sunan unguwar JABA zuwa sabuwar ENUGU a Jihar Kano.

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da sauya sunan rukunin gidaden da ke unguwar Jaba, Ƙaramar Hukumar Ungogo, zuwa New Enugu City.

A wani Rahoto da Daily Nigeria ta wallafa na Cewa Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wajen taron ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar ƴan ƙabilar Igbo mazauna Kano a unguwar Church Road da ke Kano.

Gwamna Ganduje ya ce ya ɗuu wannan matakin ne domin ƙara inganta zaman lafiya da a ke da shi a Kano, musamman tsakanin al’ummar Jihar Kano da Kuma inyamurai mazauna jihar.

“Muna jin daɗin yadda ku ke zaman lafiya da kowa a jihar nan. Ina so in sanar da ku cewa kuma ƴan Kano ne sabo da wasun ku an haife su a Kano, wasu iyaye da kakanninku ma duk a Kano aka haifesu.” Inji Ganduje.

Gwamnan ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin da su maida hankali wajen samar da zaman lafiya tsakanin ƴan ƙabilar Igbo da ma al’ummar Jihar Kano baki ɗaya, sannan kuma ya basu kyautar Naira Miliyan 5 don inganta harkokin Kungiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button