Siyasa

DA DUMI-DUMI: Kotun daukaka kara ta bayyana Sen. Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a Adamawa

Spread the love

Alkalan kotun sun bayar da umarnin mika sunan Ms Binani ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin mai rike da tutar zaben.

Kotun daukaka kara da ke Yola ta bayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Tani Hassan da Mistura Bolaji-Yusuf da James Abundaga, kotun ta yi watsi da hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta soke zaben fidda gwani na takarar gwamna tare da bayyana cewa APC ba ta da dan takarar gwamna a zaben 2023.

Alkalan kotun sun bayar da umarnin mika sunan Ms Binani ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin mai rike da tutar zaben.

A ranar 14 ga Oktoba, babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke zaben fidda gwani na takarar gwamna da ya gabatar da Ms Binani, inda ta bayyana cewa jam’iyyar ba ta da dan takara a zaben gwamna mai zuwa.

Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Nuhu Ribadu ne ya shigar da karar yana kalubalantar zaben fidda gwani na gwamnan APC kan wasu kura-kurai da aka yi, tare da neman a sake zaben fidda gwani.

Ms Binani ta samu kuri’u 430 inda ta doke abokin hamayyarta na kusa, Mista Ribadu, wanda ya samu kuri’u 288 a zaben.

Babbar kotun tarayya, a hukuncin da mai shari’a Abdulaaziz Anka ya yanke, ta ce jam’iyyar APC ba ta da dan takarar gwamna a zaben 2023 a jihar.

Mista Anka ya kuma umarci Ms Binani, wacce tun farko aka ayyana a matsayin wadda ta lashe zaben da ta daina bayyana kanta a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar a zaben gwamna na 2023.

Kotun ta bayyana cewa zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar 26 ga watan Mayu, ya ci karo da kura-kurai kamar na zabe, da rashin bin dokar zabe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button