Siyasa
Da ‘dumi ‘dumi: Yanzu-yanzu Abdulmumin Jibrin kofa ya fice daga Jam’iyar APC.


Tsohon Dan majalisar wakilai Mai wakiltar kananan hukumomin kiru da Bebeji hon Abdulmumin Jibrin kofa ya fice daga Jam’iyar APC Hon Abdulmumin ya bayyana Hakan a shafinsa na Facebook inda yake cewa yayi wa APC iya kokari na lokaci yayi da zan yi gaba. Zan sanar da sabuwar jamiyyar da zan shiga cikin sa’oi 24 In sha Allah. Zanyi cikakken bayani bada jimawa ba. Hon Abdulmumin Jibrin
Jama’a da dama na ganin Abdulmumin Jibrin zai koma jam’iyar NNPP ta kwankwaso mai kayan marmari ne Kasancewar Daman can kwankwason tsohon Mai gidansa ne.