Daga Ƙarshe, Mbaka ya bayyana, bayan ƙungiyar matasan Inyamurai ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin awa arba’in da huɗu akan a lalubo shi.

Yau ne ranar mazauna garin Enugu suka yi farin ɗango don murnar dawowar darektan ruhaniya na Adoration Ministry, Enugu Nigeria (AMEN), Rev Father Ejike Mbaka.

Jaridar The Nation da Mikiya sun rawaito cewar ansamu rashin kwanciyar hankali da zulumi a Enugu game da ɓatan malamin a ranar Laraba.

matasa masu yawa ne suka yi zanga-zanga, suna zargin cewa jami’an tsaro ko ƴan bindiga ne suka ɗauke shi saboda kiran da ya yi kwanan nan ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka ko kuma a tsige shi.

A wani bidiyo kai tsaye da aka gabatar kai tsaye a yammacin ranar Laraba da kafar yada labarai ta BBC Pidgin, wanda jaridar Mikiya ta samu gani, an ga Mbaka a cikin wata buɗaɗɗiyar mota, cike da annushuwa yana ɗaga hannu zuwa ga masu zanga-zangar da suka kewaye shi tare da jami’an rundunar ‘yan sanda ta Najeriya.


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *