Dalilin da ya sa Gwamnonin Arewa na jam’iyyar PDP sukayi yaki da Goodluck Jonathan a lokacin zabe na 2015- Daga bakin tsohon Gwamnan Niger-


Tsohon Gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu ya bayyana dalilin daya sa gwamnonin arewa na jam’iyyar PDP a baya suka yi yaki da kara zaben Goodluck Jonathan a lokaci zabe na 2015.

Aliyu ya bada haske ga wannan al’amari a inda ya bayyanawa wa jama’a dalilin yin hakan a wata sanarwa wadda ya saka hannu a ranar juma’a.

Wannan tsohon gwamna wanda PDP ta dakatar a karamar hukumar Chanchanga na jihar a dalilin yaki da yayi da sake zaben GoodLuck ya tabbatar da cewa tsofaffin gwamnonin Nigeria na Arewa sun mara wa APC baya domin tabbar da cin zaben Muhammadu Buhari.

Ya fada cewa, “Duka gwamnonin arewa da suke karkashin jam’iyyar PDP ga lokacin sun marawa Goodluck Jonathan baya lokacin da yake mataimakin shugaban kasa a yayin da yaso ida shekarun da marigayi Umaru Musa Yardua ya rasu ya bari.

“Amma, daga bisani shugaban kasa Goodluck Jonathan sai ya nemi ya yi takara a shekarar 2015 wanda wannan ya sabawa yarjejeniyar da mukayi da shi.

“Tunda haka ya sabawa yarjejeniyar da mukayi a jam’iyyar wanda mu gwamnonin arewa muka ga kamar arewar mu zata cutu idan yayi nasara sai muka mike tsaye akan lallai sai an tsaya akan yarjejeniyar da akayi.

dalilin hakan yasa muka yi hamayya da Goodluck amma daga ba nan ba, Goodluck Jonathan yaji dadin duk wani goyan bayan da arewa ta bada gareshi da nahiyar baki daya.

“Munyi hakane domin mu bi ka’ida na yarjejeniyar da akayi da Goodluck Ebele Jonathan. Wannan yarjejeniyar a rubuce take sannan kuma kowa yayi na’am da ita.

“Saboda haka ba daidai bane wani yayi kuskuren cewa ni Dr Muazu Babangida Aliyu nayi hamayya da Goodluck Ebele Jonathan.

Maryam Gidado Aminu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *