Siyasa

Doya na Siyar Tare Da Karɓar Gudummawar Kuɗi ta Naira Miliyan Ɗari (₦100, 000, 000) Daga Ƴan Uwa da Abokan Arziki Domin Siyan Fom Ɗin Takarata ta Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC — Nwajiuba

Spread the love

Ɗan takarar Shugabancin Najeriya Chukwuemeka Nwajiuba, wanda shine tsohon ƙaramin minista a ma’aikatar ilimi, ya ce kimanin ƴan Najeriya 3,150 ne suka bayar da gudunmawar kuɗi da doya domin sayen fom din takarar sa na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, wanda suka dosar ma Naira miliyan 100.
A cewar sa:

“Ina da ƴan majalisar wakilai na 1992 da suka amince da ni, tun kafin su ba da gudummawar kuɗi. Wasu sun biya Naira 1,000 kowanne. Wani mutumin Nasarawa ya ba ni doya 150 daga gonarsa in sayar. Jama’a na zuba hannun jari da fatan za a iya samun sabuwar Najeriya,” in ji tsohon ƙaramin minista, wanda ya bar muƙaminsa na gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar 10 ga watan Mayu tare da shiga takarar shugaban ƙasa.

Ɗan takarar yace ya ce burinsa shi ne ƴan Najeriya su ba da gudummawar goben su da suke so.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button