Ganduje ya karawa malaman makaranta shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano, ya karawa malaman makaranta shekarun yin ritaya.

Ya kara daga shekaru 60 zuwa 65 kuma hakan zai shafi dukkan malaman dake aiki a karkashin jihar ne.

Gwamnan yace malamai zasu iya aiki har tsawon shekaru 40 ba 35 ba kuma zai tabbatar da ingancin walwalarsu Gwamnan jihar kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kara shekarun ritaya na malaman makarantu har da na gaba da sakandare a jihar daga 60 zuwa 65.

Ganduje ya sanar da hakan ne a wata liyafar dare ta karramawa da aka yi domin bikin shagalin ranar Mayu wacce kungiyar kwadago ta jihar Kano ta shirya a ranar Asabar.

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, gwamnan ya kara shekarun aikin malaman makarantan daga 35 zuwa 40.

“Tuni gwamnatin tarayya ta amince da hakan ga malamai da kuma malaman makarantun gaba da sakanadare, hakan ne yasa ba a bar gwamnatin Kano ba a baya,” cewar ganduje.

“A don haka, daga yanzu malamai zasu fara morar sabuwar shekarar ritaya daga 60 zuwa 65 kuma zasu iya aiki na shekaru 35 zuwa 40 kamar yadda malaman tarayya ke morewa.”

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta gabatar da sabbin sauye-sauye domin inganta walwalar ma’aikatanta.

“Mun gabatar da cibiyar tarin kudi na kula da lafiyar ma’aikatanmu da iyalinsu kuma zasu mori ayyukan lafiya a cikin arha.” yace.

“Ina farin ciki da hadin kanku, a yau muna da cibiyar kula da lafiya ma’aikata mafi inganci a Najeriya.

“Muna kara hada kai da ma’aikatu masu zaman kansu a jihar domin ganin yadda zaku mora daga su a karkashin wannan hukumar tare da karfafa sabin dokokinta.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *