Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin yin amai ya lashe a kan masu garkuwa da mutane, Akan cewa “ya na nan a kan bakarsa na babu sulhu da ‘Yan bindiga”

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ya sauya ra’ayi a game da biyan kudin fansa ga ‘yan bindigan da su ke yin garkuwa da mutane.

A baya Nasir El-Rufai ya na cikin wadanda su ka azalzala wa Goodluck Jonathan a kan ya nemi sulhu domin a fito da ‘yan matan makarantar Chibok.

Bayan ya zama gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya canza akida, ya koma cikin sahun manyan wadanda ba su goyon bayan a rika biyan kudin fansa.

“Tulin kudin da ake biya a matsayin kudin fansa bayan an yi sulhu da ‘yan bindiga bai kawo karshen garkuwa da mutanen da ake yi ba.” Inji El-Rufai.

Gwamnan ya kara da cewa: “Hakan bai rage yawan barnar da ake yi ko ya taka masu burki ba.” Mai girma gwamna El-Rufai ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata ta bakin mai taimaka masa wajen yada labarai, Muyiwa Adekeye.

El-Rufai ya kare kansa, ya ce: “Hakan sai da ya kara masu kwarin gwiwa.

Abin da ya kamata shi ne mutum ya sauko daga ra’ayinsa idan bayanai sun bayyana.”

“Shawarar da mutum ya bada shekaru da su ka wuce ba za ta zama amsar shawo kan babbar matsala da ta rikida tun 2014 ba, duk yadda ake yada bidiyon.”

A ra’ayin gwamnan, sulhu da ake yi da ‘yan bindiga bai taimaka ba, sai dai ma ya jawo miyagun su ka kara karfin samun makamai da kuma kai wasu hare-haren.

Da yake magana a shafinsa na Twitter, gwamnan ya ce karen bana ne maganin zomon bana.

Daga Ahmad Aminu Kado

2 thoughts on “Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin yin amai ya lashe a kan masu garkuwa da mutane, Akan cewa “ya na nan a kan bakarsa na babu sulhu da ‘Yan bindiga”

 • April 28, 2021 at 10:24 pm
  Permalink

  Allah ya kayo mana mafuta

  Reply
 • April 28, 2021 at 10:25 pm
  Permalink

  Allah ya kayo mana mafuta. Allah ya kara tsaremu

  Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *