Gwamna Nasiru El-Rufa’i shi ne ya dace da mulkin Najeriya

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i shi ne daidai da ƴan Najeriya

Haƙika idan mu ka yi la’akari da yadda al’amura su ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya za ma ga babu wanda ya dace da mulkinta a halin da ake ciki yanzu irin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i. Idan ka ɗauki ƙasar ka saka ta a sikeli za ka ga abubuwan da suka wargazata su ne kamar haka:

1- Alfarma da nuna sanayya

A Najeriya mutum ko bai caccanci abu ba idan yana da uwa a gindin murhu sai ka ga ya samu, amma idan Nasiru El-Rufa’i ya samu shugabancin ƙasar nan zai yi mulki na babu sani babu sabo. Idan muka ɗauki loƙacin da yana ministan Abuja za mu fahimci irin yadda ya gyara birnin ba tare da nuna sani ko sabo ba. Duk gidajen manyan ƙasar nan sai daya rushe su.

Sannan, a halin yanzu ma yana gwamna duk abin da zai gudanar yana cire sanayya a cikinsa, ya lura da caccantarka.

2- Manyan Ƙasar Nan

Akwai wasu manya a Najeriya da duk shugaban da zai hau mulkin ƙasar sai ya zama ɗan amshin shatansu saboda ƙarfin ikonsu. Dan haka Najeriya tana buƙatar shugaba jajirtacce irin Nasiru El-Rufa’i wanda babu wani babba daya isa ya juya shi face sai abin da ya yi ra’ayi zai zartar.

3- Rashin Doka Da Oda

Yadda rashin doka da oda ta zama karfan ƙasa a Najeriya babu yadda za a yi ƙasar ta samu cigaban da ke buƙata. Dole ne a samu shugaban da zai tursasawa al’ummar ƙasar bin doka da oda ko suna so ko basa so. Wanda a halin yanzu babu wanda ya ke da wannan ƙarfin zuciyar da zai yi haka kamar Gwamna Nasiru El-Rufa’i

4- Ta’addanci

Babban ƙalubalen Najeriya a halin yanzu bai wuce yadda ta’addanci ya yiwa ƙasar ƙawanya ba, wanda akwai hanyoyi da yawa da za a bi wajan magance shi, daga cikin wanda masana su ke faɗa akwai lugudan wuta a dajin Sambisa, amma sakamakon idan aka yi haka hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya za ta zargi ƙasar akan ta kashe fararen hular da su ke cikin dajin shi yasa har yanzu hakan bata samu ba

Amma tabbas idan Nasiru El-Rufa’i ya zama shugaban ƙasa zai rufe idonsa ya yi abubuwan da suka dace saboda mun ga yadda ya kwatanta hakan a jiharsa ta Kaduna. Idan ban da Allah Ya sa shi ne gwamnan jihar da yanzu rikice-rikicen ƙabilanci sun cigaba da afkuwa.

Saidai duk da haka, akwai ƴan kura-kurai dayakamata ya gyara kamar korar ma’aikata da sauransu.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *