Gwamnan Yobe Ya Gana da Shugaban Hafsoshin Tsaro Kan Batun Boko Haram a Geidam

Gwamna Buni ya gana masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya a yankin Geidam – Gwamnan ya tattauna da shugaban hafsoshin tsaro kan mafita mai dorewa ga lamarin tsaro – Gwamnan ya bayyana cewa, dole ne a matsayinsa na jagora ya nemo hanyoyin magance tsaro KU KARANTA:

‘Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, a ranar Lahadi ya gana da shugaban hafsoshin tsaro Janar Leo Irabo don tattauna batun harin Boko Haram a Geidam.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na harkokin yada labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, Vanguard News ta ruwaito. Mohammed ya ce, tun daga ranar Juma’a ne Buni ya kasance yana tattaunawa da jami’an tsaro don samar da mafita mai dorewa game da kai hare-hare a kan Geidam da al’ummomin kan iyaka.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *