Gwamnatin Tarayya Za Ta Kori Ma’aikata Da Ba Su San Makamashin Aiki Ba

Gwamnatin tarayya ta nuna alamar tana shirin korar ma’aikata da ba su san makamashin aiki ba –

Folashade Yemi-Esan, shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ce ta sanar da hakan ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu –

Shugaban ma’aikatan na kasa ta ce wadanda suka cancanta ne kawai za a dauka aiki a hukumomin gwamnatin tarayya Folashade Yemi-Esan, shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, HoS, ta ce za a bullo da tsarin da zai tabbatar wadanda suka dace ne kawai za su samu aikin gwamnatin tarayya.

Vanguard ta ruwaito cewa Yemi-Esan ta yi wannan furucin ne a wurin taron Hukumar Yin Sauye-Sauye a ayyukan gwamnati, BPSR, da aka yi a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu a Abuja.

Ta ce akwai bukatar a yi waje da wadanda ba su san makamashin aiki ba.

Emmanuel Meribole, Sakataren dindindin na bangaren tsare-tsare a ofishin na HoS ne ya wakilci Yemi-Esan a wurin taron.

A cewarta, a halin yanzu gwamnatin tarayya ba hukuma bace da za a rika daukan ko wane irin mutane aiki domin magance matsalar rashin ayyuka a kasar.

HoS din ta ce aikin gwamnatin tarayya na kan tsari ne na magance matsalar tattalin arziki, zamantakewa da muhalli na SDGs.

Shugaban BPSR, Dasuki Arabi ya ce bayan annobar COVID-19, ana bukatar aiwatar da sabon tsarin aikin gwamnati na zamani da gwamnatin tarayya ta tsara.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *