Siyasa

Idan dai Kuna jin kun Isa ku Hanani na zama shugaban Kasar Nageriya a zaben 2023 ~Sakon Atiku ga gwamnonin PDP na G-5

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce duk wanda ke shirin hana shi cimma burinsa na siyasa, to ya fara mayar da kansa shugaban Najeriya.

Hakazalika tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa bai damu da makircin wasu gwamnoni biyar da aka fi sani da G-5 ba, bisa zabin su na ‘yan takarar shugaban kasa da suke so ba.

Ya bayyana cewa shi giwa ne da ya ga komai, yana mai cewa ba za a yi mamakin yadda gwamnonin suka yi masa ba.

Atiku, wanda ya yi magana ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya ce duk wanda ke takama da cewa yana da irin wannan iko na dakatar da takararsa na shugaban kasa, to ya fara zama shugaban kasa.

Kalamansa: “Atiku zai zama shugaban kasa. Ko zakara ya yi cara, dole ne rana ta fito. Iko na Allah madaukaki ne; babu wani mutum da zai iya girman kan kansa da ikon Allah madaukaki. Duk mutumin da zai yi takama da hana Atiku ya fara maida kansa shugaban Najeriya.

“Atiku giwa ne. Ko da giwa ta yi tafiya a kan ƙaya hakan baya rage mata komai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button