Siyasa

Jam’iyyar Labour za ta kawo karshen rashin tsaro idan aka zabe mu – Datti Baba-Ahmed

Spread the love

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce jam’iyyarsa za ta kawo karshen kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya idan har aka zabe su ta karbi ragamar shugabancin kasar a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.

Ya yi wannan alkawarin ne a wata hira da wasu zababbun ‘yan jarida a Sokoto inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar Labour za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Ya ce jam’iyyarsa za ta dogara ne kan fasahar kere-kere tare da hada hannu da masu ruwa da tsaki don ganin an kare kowace murabba’in mita a cikin yankin Najeriya tare da dakile hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami.

Baba-Ahmed ya kuma yi alkawarin cewa jam’iyyarsa za ta juya tattalin arzikin kasa tare da kame hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar shirye-shirye da tsare-tsare da gangan sakamakon gogewa da masaniyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi kan harkokin tattalin arziki.

Baba-Ahmed ya ce rikicin da ke kunno kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Ma’aikatan Jami’a, za a magance shi ne a lokacin da Jam’iyyar Labour ta karbi ragamar mulkin kasar nan, domin kuwa ilimi za a bai wa fifiko a gwamnatinsu.

Channels TV

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button