Ka Sauka Kayi Murabus Kawai, Martanin Jam’iyyar PDP Ga Pantami.

Jam’iyyar PDP ta nemi Ministan Sadarwa da tatalin Arziki, Sheikh Isa Ali Pantami yayi Murabus daga mukaminsa saboda kalaman goyon bayan Alqaeda da Taliban da yayi a baya.

Hakan na zuwane duk da Ministan yayi bayanin cewa yayi wadancan kalaman ne lokacin yana karamin yaro amma da ya girma, hankali ya shigeshi kuma ya kara ilimi,Tuninsa ya canja.

Shugaba PDP, Uche Secondus ne ya bayyana haka a wata Ganawa da Punchng inda yace Pantamin ya sauka dan bai cancanci rike mukamin ba kuma ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri.

Yace bayan ya sauka yana iya fara wa’azin adawa da ayyukan kungiyoyin ta’addanci a bainar jama’a dan a shaida.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *