Kara Farashin Man Fetur A Najeriya Zallar Zalinci Ne, Inji Kawu Mashawarcin Buhari Na Da.

Tsohon mai bawa shugaban kasa muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisar tarayyar Hon. Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya kalubalanci ‘yan kishin kasa da wadanda ya kirawo magoya bayan Buhari na hakika, da kuma ‘yan jam’iyun adawa kan lallai ya zama wajibi su nuna rashin amincewar su da yin Karin farashin manfetur din a Najeriya.

Hon kawu sumaila ya bayyana cewa dole ne ‘yan kasa suyi bore akan wannan karin na farashin man fetur din a Najeriya, domin kuwa duk inda za aje adawo Karin akan talakawan zai kare.

Hon. Kawu Sumaila na daya cikin jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar APC, haka kuma ya taka rawar gani wajen kafuwar gwamnatin shugaba Buhari a shekarar 2015.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published.