Siyasa

Kawo yanzu na tallafawa da gidajen iyalai dubu goma sha biyu 12,000 da samun damar lamuni daga Babban Nageriya CBN ~Cewar Sanata Uba sani.

Spread the love

Sanatan ya bayyana hakan ne a farkon wannan watan a yayin ganarwarsu da kungiyar ‘yan kasuwar Arewa tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Kaduna daga dukkanin kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar Wanda suka bayyana goyon bayansu ga takararsa da Kuma takarar dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed, dama sauran yan takarar APC a zaben baɗi.

Sanatan Yana cewa a Lokacin taron na tabo wasu daga cikin irin kokarin da nayi a matsayina na Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, kuma a matsayina na Shugaban kwamitin Bankunan Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, inda ya bani dama na taimaka wa al’ummai ta hanyar Babban Bankin kasa CBN, wajen taimaka wa gidaje sama da 12,000 ta Shirin nan na SMEs da tallafi ba lamuni don bunkasa sana’o’insu sakamakon annobar COVID-19 bisa la’akari da Matsin akan tattalin arziki.”

A Lokacin taron Sanatan yace Domin samun ci gaba da kokarin gwamnatin jihar Kaduna da ta riga ta gina manyan kasuwanni na zamani, na tallafa wa ’yan kasuwa masu tasowa da kudi Naira Miliyan Ashirin (N20,000,000) wanda zai taimaka musu wajen samun kashi 10% na hannun jari don mallakar shaguna a kasuwanni a fadin jihar.”

Sanata Uba sani Dan takara mafi karfi a cikin Yan takarar Neman Gwamnan jihar Kaduna ya samu shedar taimakon talakawan dayake wakiltar na Kaduna tsakiya dama al’ummar jihar Kaduna Kai harma da matakin kasa Baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button