Ku ajiye siyasa a gefe ku yiwa Buhari addu’a- Tinubu

IDIN SALLAH ƘARAMA: Ku Ajiye Siyasa gefe, ku yi wa Buhari Addu’a, Tinubu Ya Nemi Ƴan Najeriya

Jagoran APC na kasa, Tinubu ya ce, “Kada mu yi la’akari da kalaman wasu ɓata garin ƴan siyasa a kan buhari kamata yayi mu duƙufa da yi mishi addu’a dan ganin cewa nijeriya ta samu tabbataccen zaman lafiya da yalwar arziƙi a ƙasa.

Tinubu, Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su ajiye siyasa a gefe su ci gaba da yi wa Buhari da gwamnatinsa addu’a da fata nagari.

Yana mai cewa Mu tuna da Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa a cikin addu’o’inmu don su samu ƙarfin da ake buƙata da hikima wajen kare al’umma, da kayar da ƙalubalen da ke gabanmu da kuma taimakawa kafa Nijeriya a matsayin ƙasa mai wadata da adalci,” in ji shi.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *