Ku miƙa wuya cikin kwanaki huɗu ko ku haɗu da fushin gwamnati- gargaɗin gwamna Matawalle ga ƴan bindiga

Cikin kwanaki huɗu ku miƙa wuya ko kuma ku fuskanci fushin gwamnati -Gargaɗin Matawalle ga ƴan bindiga

Matawalle na jihar Zamfara ya zargi wasu ƴan bindiga da yaudara gwamnati Gwamnan ya ce ya samar da wata sabuwar dabara ta tsaro domin kiyaye mazauna yankin. Ƴan bindiga sun mamaye wasu garuruwa a jihar ta Zamfara tare da hallaka mutane da dama Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya gargadi ƴan bindiga a jihar da su tuba ko kuma su fuskanci mummunan mataki daga gwamnati.

Gwamnan a ranar Asabar 24 ga Afrilu, ya bayyana cewa ya tsara sabuwar taswira a yadda yake tunkarar matsalar tsaro da ke addabar jihar, a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa Malam Yusuf Gusau wacce gidan talabijin Channels TV ta ruwaito. Matawalle ya bayyana cewa dakatarwar da aka yiwa wani hakimi a masarautar Shinkafi kwanan nan saboda haɗa kai da ƴan bindiga yana ɗaya daga cikin sababbin matakan da ya yanke shawarar aiwatarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *