Kusa A ranku Cewa Nijeriya Zata Samu Zaman Lafiya A karkashin Gwamnati Na, “Inji Buhari

Ayau shugaban Najiriya Muhammadu buhari ya kara lashan takobin cewa zai kawo karshen matsalar tsaron da ya addabi Nijeriya insha Allahu.

Shugaban kasa Buhari ya yi wannan furicin ne a daidai lokacin da yake Allah wadai da kisan daliban jami’ar Greenfield da masu garkuwa da mutane suka sace kwanaki 3 da suka gabata a makarantarsu dake jihar Kaduna.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa wannan hare-hare da kashe-kashen da ake yi a jihar Kaduna abin takaici ne.

A jawabin da shugaba buhari ya saki a ranar Asabar a Tuwita, ya lashi takobin cewa sai gwamnatinsa ta kawo karshen wadannan yan bindigan da dukkan masu aikata ta,addanci a cikin Nijeriya.

Muna Rokon Ubangiji Allah ya taimaki shugaban Najiriya Muhammadu buhari ya akan kyawawan manufufin shi na alkairi.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *