Siyasa

Lafiyar Tinubu: Duk Wani Dan Najeriya Da Ya Haura Shekara 40 Ba Shi Da Lafiya – Orji Kalu

Spread the love

Dan majalisar tarayya ya kuma ce wasu kalamai marasa daidaituwa da aka danganta ga Tinubu, ‘yan adawar siyasa ne suka kirkiro su.

Babban mai shigar da kara na majalisar dattawa, Orji Kalu ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC a 2023, Bola Tinubu ba shi da matsalar lafiya.

Kalu, wanda tsohon gwamnan jihar Abia ne ya kuma kara da cewa duk wani dan Najeriya da ya haura shekaru 40 yana fama da matsalar rashin lafiya.

“Lafiyarsa (Tinubu) tana da kwanciyar hankali. Duk mutumin da ya wuce 40 ba shi da lafiya. Babu dan Najeriya me sama da 40 yake da lafiya,” in ji Kalu a cikin Political Paradigm, wani shiri da aka nada a gidan Talabijin na Channels.

Dan majalisar na tarayya ya kuma ce wasu kalamai marasa daidaituwa da aka danganta ga Tinubu an yi su ne wajen tarukan ‘yan adawa ne na siyasa.

“Waɗannan abubuwa ne da ku mutane za ku je ku kafa ta intanet. Duk wadannan abubuwa ‘yan adawa ne na siyasa za su iya kirkiro su,” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button